Event:Hausa Community Wiki For Human Rights 2025
WikiForHumanRights 2025 a Najeriya (Hausa Community)
Sanin Hakkokin Dan Adam Don Makoma Mai Dorewa
Maris zuwa Mayu 2025
[Social media: #WikiForHumanRights #WikiDodinDanAdam #HausaWiki]

Gabatarwa
[edit]WikiForHumanRights yana da nufin haɓaka abubuwan da suka shafi hakkokin dan adam a cikin harshen Hausa ta hanyar ƙarfafa al’umma wajen bayar da gudummawa a shafukan Wikimedia kamar Hausa Wikipedia, Wikidata, Wikimedia Commons da sauransu. Wannan aiki yana mai da hankali ne kan "Sanin Hakkokin Dan Adam don Makoma Mai Dorewa".
Za a gudanar da wannan aiki a cikin arewacin Najeriya inda ake da yawan masu amfani da harshen Hausa, tare da hada da tarurruka, bitoci da kuma gasar gyara ko ƙirƙirar sabbin makaloli.
Abubuwan Da Za Ayi
[edit]Me
[edit]- Taron horarwa akan yadda ake gyara Wikipedia, Wikidata, Commons da sauransu
- Gasar ƙirƙira da gyaran makaloli akan hakkokin dan adam a cikin Hausa
- Samun jagorori da za su ci gaba da horas da sababbin masu gyarawa
- Haɗin gwiwa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam da jami'o'i
Yaushe
[edit]Aikin zai gudana ne daga watan Maris zuwa watan Mayu 2025.
Ta yaya
[edit]- Za a horar da mahalarta kan dabarun gyaran makaloli da amfani da ka’idojin Wikimedia
- Za a buɗe gasa ta musamman don sabbin da tsoffin masu gyarawa su ƙirƙira ko inganta makaloli, bayanai da hotuna
- Za a yi amfani da kayan aiki kamar Wikimedia Dashboard don tantance tasirin aikin
Su waye za su halarta?
[edit]- Duk wani mai sha’awar batutuwan haƙƙin ɗan adam
- Sabbin da tsoffin masu gyara a Wikipedia da sauran wuraren Wikimedia
- Ƙungiyoyin matasa, dalibai, ƙungiyoyin fararen hula da masu rajin kare haƙƙin ɗan adam
- Kowa da kowa da ke iya bayar da gudummawa a cikin harshen Hausa
Me yasa?
[edit]- Don ƙara yawan abubuwan da suka shafi haƙƙin ɗan adam a cikin Hausa
- Don wayar da kan jama'a game da muhimmancin hakkin ɗan adam
- Don baiwa masu magana da harshen Hausa damar samun ingantattun bayanai akan hakkokinsu
- Don gina ƙungiyar wikimediyoyin Hausa da ke da ƙwarewa akan batutuwan haƙƙin ɗan adam
Gasa
[edit]Akwai gasar rubutu game da Maƙalolin da suka shafi take shirin Wiki For Human Rights na Bana wadda za'a ci manyan kyaututtuka. Ƙarin bayani a game da gasar yana nan zuwa...
Abubuwan da ake sa ran samu
[edit]- Ƙirƙirar da gyaran makaloli sama da 1000 a Hausa Wikipedia akan batutuwan haƙƙin ɗan adam
- Ƙara sabbin bayanai a Wikidata masu nasaba da haƙƙin ɗan adam
- Ɗora hotuna da kayan gani masu nasaba da batutuwan haƙƙin ɗan adam a Wikimedia Commons
- Kafa ƙungiyar sabbin masu gyarawa da ke da horo kan batun
Kyaututtukan da za'a Iya ci a gasa
[edit]Za a bayar da lambobin yabo kamar haka:
| Matsayi | Kyauta (a Kuɗi) | Bayani |
|---|---|---|
| 🥇 Na Farko | ₦100,000 | Mafi yawan gudummawa tare da inganci |
| 🥈 Na Biyu | ₦70,000 | Na biyu mafi yawan gudummawa mai amfani |
| 🥉 Na Uku | ₦50,000 | Na uku a cikin masu kokari |
| Top 10 (Sauran bakwai) | ₦5,000 kowanne | Kyautar godiya ga kwazon su |
Ma’aunin Gasa/Tsarin Maki
[edit]Ana bayar da maki kamar haka:
Ƙirƙirar Sabuwar Maƙala:
maki 10: Ƙirƙirar sabuwar maƙala da ta kai aƙalla 4000 bytes (haruffa 4000)
maki 8: Ƙirƙirar sabuwar maƙala da ta kai aƙalla 3999–3000 bytes (haruffa 3999–3000)
maki 8: Ƙirƙirar sabuwar maƙala da ta kai aƙalla 2999–2000 bytes (haruffa 2999–2000)
maki 4: Ƙirƙirar sabuwar maƙala da ta kai aƙalla 1999–1000 bytes (haruffa 1999–1000)
maki 3: Ƙirƙirar sabuwar maƙala da ta kai aƙalla 999–500 bytes (haruffa 999–500)
maki 2: Ƙirƙirar sabuwar maƙala da ta kai aƙalla 499–100 bytes (haruffa 499–100)
maki 1.5: Ƙirƙirar sabuwar maƙala da ta kai aƙalla 99–50 bytes (haruffa 99–50)
maki 1: Ƙirƙirar sabuwar maƙala da ta kai aƙalla 49–1 bytes (haruffa 49–1)
Bunƙasa Maƙala:
maki 8: Bunƙasa maƙala ta ta kai aƙalla 4000 bytes (haruffa 4000)
maki 6: Bunƙasa maƙala ta ta kai aƙalla 3999–3000 bytes (haruffa 3999–3000)
maki 5: Bunƙasa maƙala ta ta kai aƙalla 2999–2000 bytes (haruffa 2999–2000)
maki 3: Bunƙasa maƙala ta ta kai aƙalla 1999–1000 bytes (haruffa 1999–1000)
maki 2: Bunƙasa maƙala ta ta kai aƙalla 999–500 bytes (haruffa 999–500)
maki 1.5: Bunƙasa maƙala ta ta kai aƙalla 499–100 bytes (haruffa 499–100)
maki 1: Bunƙasa maƙala ta ta kai aƙalla 99–50 bytes (haruffa 99–50)
maki 1.5: Bunƙasa maƙala ta ta kai aƙalla 49–1 bytes (haruffa 49–1)
Lura: Za ka iya amfani da kayan aikin ƙididdigar haruffa don duba yawan bytes ko haruffa da ka ƙara a cikin labarinka.
Yadda za a shiga
[edit]Fara
Mataki na 1: ko kuma:Mataki na 2: |
Hotuna daga aikin
[edit]Hotunan tarurruka da bitoci za su kasance a: Wiki For Human Rights 2025 in Hausa Community Events



