Taro:Bajen Kolin Kungiyar Wikipedia da ILimi/Mayun 2026
<Wikipedia & Education User Group

Baje kolin Ilimantarwa na EduWiki wani sarari ne na tallafawa jama'a wanda ke samar da dandali na daidaito ga membobin Kungiyar Wikipedia da Ilimantarwa, da kuma masu koyarwa da kuma editocin Wikimidiya a duk fadin duniya, don baje kolin ayyukan Wikimidiya na ilimantarwa, harkoki, wuraren karawa juna sani, ko kuma abubuwan nazari game da dabarun ilimantarwa. Har wayau, yana samar da sarari ga mambobin al'ummar EduWiki don sadarwa da koyo ta yanar gizo.
Wannan sashi na March 2026 zai haska dabarun Wikimidiya ta ilimantarwa a yankunan ESEAP, CEE, da kuma MENA. Masu gabatarwa Anton Protsiuk, mai Shirya Shirye-shirye a Wikimedia Ukraine, da kuma Dr. Walaa Abdel Manaem,, Malami kuma Jagorar Wikimidiya a Jami'ar Cairo, zasu yada basirori daga shirye-shirye daga kasashen su bi da bi, tare da mayar da hankali a kan hanyoyin dabaru wajen ilimantarwa daga Wikimidiya da kuma mu'amalantan jama'a.
Har ila yau, sashen zai ƙunshi gabatarwar fasaha daga membobin al'umma, tare da bayar da fage don bada gudummawa a takaice, wanda zai assasa bayar da gudummawa. Wadanda suka halarci taron za su sami damar koyo, yin tambayoyi, da musayar ra'ayoyi game da inganta ilimi da janyo jama'a ta hanyar ayyukan Wikimedia.
Bayanai
- Date: 24 Maris 2026
- Time: 13:00 UTC
- Location: Zoom
- Tallafawa wajen fassara na kai-tsaye: Harshen Potugis, Faransanci, Sifaniyanci, Harshen Hindi, Larabci, Harshen Indunusiya