Ƙungiyar Masu amfani da Wikimediya ta Hausa

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki
This page is a translated version of the page Hausa Wikimedians User Group and the translation is 100% complete.
HAUSA WIKIMEDIANS USERGROUP




Ƙungiyar Masu Amfani da Wikimedia ta Hausa (An kafa da yi mata rijista da Gidauniyar Hausa Wikimedia; CAC/IT/192786 a Najeriya) ƙungiya ce mai zaman kanta da ta sadaukar da kanta don inganta ayyukan Wikimedia, tare da mai da hankali ta musamman a Harshen Hausa da batutuwa da suka shafi' mutane, al'adu, zamantakewarta, tarihi da bayan Haka, muna taimakawa, ƙarfafawa da ilimantar da masu amfani da yaren Hausa da al'ummomi kan muhimmancin buɗaɗɗiyar fasaha, musayar ilimi da sauran shirye-shiryen ilimantarwa ta hanyar horo da abubuwan da ƙungiyar ke shiryawa. Kasancewa mamba a buɗe take ga mutane masu sha'awa da ra'ayi iri ɗaya da namu, ƙungiyar yanke shawara ita ce Kwamitin Amintattu.

Manufofi

  • Domin ciyar da ayyukan Wikimedia gaba
  • Don inganta gyaran Wikipedia da sauran ayyukan Wikimedia duka a cikin Hausa da sauran harsuna.
  • Don shiga tare da ƙarfafawa masu magana da harshen Hausa don zama masu bada gudummawa a ayyukan Wikimedia.
  • Don shirya taruka ga Wikipedians/Wikimedians na gida ta hanyar samar musu da kayan aikin da ake buƙata don haɓaka ƙwarewar su da ƙwarewar ci gaban ayyukan Wikimedia.

Ayyuka

Wannan ƙungiyar ta masu amfani tana bada goyon baya ga wannan ayyukan:

  • Taruruka rukunin masu amfani zasu shirya taron ganawa ga mambobinta domin musayar ra'ayoyi da nemo hanyoyin tallafa musu don ci gaba da gyara ayyukan a wuraren da zasu buƙaci taimako.
  • Edit-a-thons don taimakawa sabbin Wikipedians don koyon fasahohin gyara, don ƙirƙira, fassarawa da haɓaka abubuwan cikin duk ayyukan Wikimedia ko aiki a kansu da haɓaka wani batun wanda zai dawo da aikin.
  • Gasar rubutu rukunin za su shirya gasa masu gyara don ƙarfafa editocin yau da kullun su ci gaba da gyara ayyukan Wikimedia da kuma ƙarfafa waɗanda ba membobi ba/masu amfani su shiga.
  • Gasar daukar hoto da tafiye-tafiye ƙungiyar za ta kuma shirya tafiye-tafiye da gasa don karfafa masu amfani don lodawa da kuma rubuta fayilolin zuwa tarukan da za a yi amfani da su a duk ayyukan Wikimedia.

== Kwamitin Haɗin kai/Alaƙa Ƙudiri

Bayanan Tuntuɓa

Tuntuɓe mu
contact@wikimediahausa.org
Rukunin imail
Shiga jerin imail din mu wikimedia-ha@lists.wikimedia.org

 Official website Mailing list