Universal Code of Conduct/Bitar shekara-shekara/Saƙonni/An buɗe bita
Ina rubuto maka ne domin sanar da kai cewa an buɗe lokacin bitar shekara-shekara na Universal Code of Conduct da Ka’idojin Aiwtarwa. Kana iya ba da shawarwari kan sauye-sauye har zuwa 9 ga Fabrairu, 2026. Wannan shi ne mataki na farko cikin jerin matakai da za a ɗauka domin bitar shekara-shekara. Karanta ƙarin bayani kuma ka samu tattaunawa da za ka shiga a shafin UCoC a Meta.
The Kwamitin Daidaita Aiwatar da Universal Code of Conduct (U4C) wata ƙungiya ce ta duniya da ta sadaukar da kai wajen tabbatar da adalci da daidaitaccen aiwatar da UCoC. Wannan bitar shekara-shekara an tsara ta kuma an aiwatar da ita ne ta hannun U4C. Don samun ƙarin bayani da kuma fahimtar nauyin da ke kan U4C, kana iya duba Kundin Tsarin U4C.
Da fatan za a raba wannan bayanin zuwa ga wasu mambobi a cikin al'ummarku inda ya dace.
-- A cikin haɗin gwiwa da U4C, Keegan (WMF) (tattaunawa)