Jump to content

Gamayyar Tsarin Gudanarwa/Tattaunawa/Mahukunta Q&A 2023

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki
This page is a translated version of the page Universal Code of Conduct/Conversations/Panel Q&A 2023 and the translation is 100% complete.

Kungiyar Amintattun Gidauniyar Wikimedia da Manufofin Tsaro za su karbi bakuncin Panel Q&A tare da membobin al'umma a ranar 15 ga Janairu 2023 a xx UTC don tattauna Tsarukan Tirsasawar Gamayyar Tsarin Gudanarwa (UCoC) da kuma buƙatar shigar al'umma a cikin ƙuri'ar Rattabawa mai zuwa. Wani muhimmin abin da za a mayar da hankali kan taron shi ne dalilin da ya sa yake da muhimmanci ga kananan da matsakaitan al'ummomin Wikimedia su shiga cikin kuri'ar rattabawa.

'Yan majalisa sune: Uzoma Ozurumba, Tanveer Haasan, Ruby Damenshie-Brown, da Claudia Lo.

Wannan taron wani bangare ne na kokarinmu na shiga, ilmantarwa da sanar da al'ummar Wikimedia game da UCoC, Tsarukan Tirsasawa da kuma zaben Rattabawa na UCoC mai zuwa.

Muna rokonka da ka gayyato sauran masu sa kai a cikin al'ummarka don sanar da su da kuma ba su damar yin zabe! Da fatan za a yi rajista a nan ko aika imel ucocproject@wikimedia.org idan kuna son halarta.