Jump to content

Tallafi:Shirye-shirye/Asusun Al'umma na Wikimedia/ Sabunta Asusun tallafin gaggawa (2022)

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki
This page is a translated version of the page Grants:Programs/Wikimedia Community Fund/Rapid Fund updates (2022) and the translation is 99% complete.


Sabuntawar tsarin tallafin gaggawa (2022)

Muna sanar da cewar mun yi sauye-sauye a tsarin tallafin gaggawa na wanda ya danganci zangon tallafi, iyakar tallafi da kuma tsarin neman tallafi. Canje-canjen sun daidaita kuma suna goyan bayan ci gaba da fahimtar sabon shiri na Tsare-tsaren tallafi na Gidauniyar Wikimedia da kuma mayar da hankali ga ba da damar yanke shawara, kwamitocin yanki da kuma isa ga al'ummomin da ba su da wakilci. Muna ci gaba da yin amanna cewa canje-canjen za su magance buƙatun al'umma kuma su motsa mu zuwa ga tabbatar da abubuwan dabarun shugabanci

Me ya jawo wadannan sauye-sauyen

Munga karin yawan masu neman tallafi na gaggawa daga sababbin ƙasashe da kuma ƙarin masu gudunmawa ga tafiyar da albarkatun data kasance da kuma sababbin himma. Muna son ci gaba da tallafawa shirin da haɗin kai da haɗin gwiwa tsakanin al'ummomi daban-daban. Mun yi la'akari da iyawar da ake da su, albarkatun da ake da su da kuma manufar Kuɗaɗen gaggawa don samar da sauƙi da saurin samun kuɗi.

Menene sauye-sauyen

Muna gabatar da waɗannan sauye-sauyen;

  • Tsarin Lokaci:
    • Mun ƙara tsarin zagayen lokaci daga kwanaki 30 zuwa 45. Duba tsarin lokacin domin sauran kalandar shekara.
  • Iyakar tallafi:
    • Mutane na da damar neman tallafi sau biyu kacal a ko wanne lokaci. Adadin kuɗin da za'a bawa ɗaiɗaiku ba zai wuce Dalar Amurka 10,000 ba, ana ƙarfafawa masu neman tallafin don matsawa cikin shirin na dogon lokaci a cikin Shirin Tallafin Gabaɗaya lokacin da ake buƙatar ƙarin albarkatu.
    • Ƙungiyoyin da suka haɗa da masu alaƙa da Wikimedia da ƙungiyoyin da aka tsara masu zaman kansu za a iyakance su zuwa buɗaɗɗun tallafi guda 3 a kowane lokaci. Jimlar ƙimar tallafin ƙungiya da ƙungiyoyi za su iya shiga kowace shekara za ta kai dalar Amurka 10,000. Muna ƙarfafa masu nema don matsawa cikin shirin dogon lokaci a cikin Asusun Tallafawa Gabaɗaya inda ake buƙatar ƙarin albarkatu. Wannan kuma ya shafi ƙungiyoyin da ba na yau da kullun waɗanda membobinsu ke neman Rapid Funds a matsayin daidaikun mutane (Wiki Fan Clubs, kulab ɗin jami'a, Ƙungiyoyin Masu amfani da aka tsara, da sauransu.)
  • Za a yi amfani da aikace-aikacen da aka sake sabuntawa da fom ɗin rahoto za a yi amfani da su akan Fluxx Grantee portal,
    • Tsarin kula da tallafin da ake amfani da shi a halin yanzu a cikin sauran shirye-shiryen bayar da kuɗi. Masu nema har yanzu za su yi hulɗa tare da membobin Community akan meta kamar yadda duk aikace-aikacen za a buga ta atomatik akan Meta. Aikace-aikacen da aka yi daga 15 ga Afrilu za a yi su ta hanyar Fluxx, har sai masu neman za su ci gaba da amfani da hanyar nema ta yanzu a kan Meta.
  • Haɗin kan al'umma:
    • Za mu bada jagoranci ga membobin kungoyin al'ummomi kan yadda za su ba da tsokaci mai ma'ana ga tsarin tallafin masu nema ta hanyar yin takamaimun tambayoyi a shafukan tattaunawa waɗanda suka shafi:
      • Tasirin aiki
      • Daidaita tasiri da agajin da ake nema
      • sababbin ra'ayin ci gaban aiki
      • Ƙarfin aiwatar da ayyuka

Manufar mu ita ce ƙarfafa tsari na yanzu na ba da tallafi ga ayyukan da aka gabatar.

  • Kwamitocin yanki za su goyi bayan tsarin bita na shawarwarin bayar da gudummawar da ke ba da ra'ayi mai ma'ana da jawo hankali don ƙarfafa tsarin tallafi da kuma nuna damammaki don haɗin gwiwa da haɗin kai tsakanin membobin al'ummomi.
  • Jami'an shirin za su goyi bayan yunƙurin ƙarfafawa masu haɗin gwiwar manufa don yin aiki tare da juna a kan ayyuka da kuma abokan haɗin gwiwa da gogaggun editocin Wikimedians don tallafawa sababbin masu zuwa gwargwadon yiwuwar.
  • Masu neman za su buƙaci raba rahotannin ayyukan da suke bayarwa tare da mahalarta da membobin al'umma suna samar da dama don raba abubuwan ilmantarwa tare da wasu kuma don membobin al'umma su raba ra'ayoyinsu.

Taya Canjin zai kasance

Duk canje-canjen da aka ambata za su fara aiki daga 15 ga watan Afrilun 2022. Lura cewa waɗannan canje-canjen ba sa tasiri ga duk wanda ke da tallafi mai gudana.

Za mu sami lokutan ganawa (duba a ƙasa) don gabatar da canje-canje ga al'ummomi da tallafawa canjin. Sabon Mu Haɗa Shirin Koyo na Abokin Zamani kuma za a sami zaman koyo don tallafawa masu ba da tallafi kan buƙatu daban-daban na tushen ƙarfi.

A nan mun saka sabon aikace-aikacen don fara dubawa

Anan mun saka Rijistar Fluxx da portal.

Mun fahimci cewa duk waɗannan canje-canje na iya zama sabon abu. Muna nan don tallafa muku, don haka don Allah kar ku yi jinkirin tuntuɓar jami'in shirye-shiryen yanki ko halartar ɗaya daga cikin sa'o'in ofis ɗin da aka tsara.

Muna gode maku bisa ga yadda kuke bamu haɗin kai a yayin da muke cigaba da gudanar da tsare-tsaren yadda muke bayar da tallafin mu, koyi da sake maimaita bayanin ta hanyar ra'ayoyin da kuka raba tare da mu.

Mun gode

Tsarin lokuta

Afrilu-Mayu

Zagaye na 1: Afrilu 15 - Mayu 31
Kwanakin wata na Tallafin gaggawa Aiyuka Ƙiyasin lokaci
Afrilu 15 2022 Ƙarshen lokacin miƙa neman tallafi
Afrilu 16 - 29 2022 Dubawa da mayar da martani na neman da aka miƙa kwanaki 14
Afrilu 30 - Mayu 9 Mai nema zai karɓa kuma zai yi aiki tare da amsa shawarwari daga al'umma da kwamitin yanki Kwanaki 10
Afrilu 30 - Mayu 9 Masu nema za su yi ƙari ga neman tallafin su idan akwai bukatar hakan Kwanaki 10
Mayu 10 - Mayu 24 Amincewa da bayarwa Kwanaki 14

Yuni-Juli

Zagaye na 2: 1 Yuni - Yuli 15
Kwanakin wata na Tallafin gaggawa Aiyuka Ƙiyasin lokaci
Yuni 1 2022 Ƙarshen lokacin miƙa neman tallafi
Yuni 2 - 15 2022 Dubawa da mayar da martani ga neman da aka miƙa Kwanaki 14
Yuni 16 - 25 Mai nema zai karɓa kuma zai yi aiki tare da amsa shawarwari daga al'umma da kwamitin yanki Kwanaki 10
Yuni 16 - 25 Masu nema za su yi ƙari ga neman tallafin su idan akwai bukatar hakan Kwanaki 10
Yuni 26 - Yuli 10 Amincewa da bayarwa Kwanaki 14

Yuli-Augusta

Zagaye na 3: Yuli 15 - Augusta 31
Kwanakin wata na Tallafin gaggawa Aiyuka Ƙiyasin lokaci
15 Yuli 2022 Ƙarshen lokacin miƙa neman tallafi
Yuli 16 - 29 2022 Dubawa da mayar da martani ga neman da aka miƙa Kwanaki 14
Yuli 30 - 8 Augusta Mai nema zai karɓa kuma zai yi aiki tare da amsa shawarwari daga al'umma da kwamitin yanki Kwanaki 10
Yuli 30 - 8 Augusta Masu nema za su yi ƙari ga neman tallafin su idan akwai bukatar hakan Kwanaki 10
9 Augusta - 22 Augusta Amincewa da bayarwa Kwanaki 14

Satumba-Oktoba

Zagaye na 4: 1 Satumba - Oktoba 15
Kwanakin wata na Tallafin gaggawa Aiyuka Ƙiyasin lokaci
1 Satumba Ƙarshen lokacin miƙa tallafi
2 - 15 Satumba Dubawa da mayar da martan da neman da aka miƙa Kwanaki 14
16 - 15 Satumba Mai nema zai karɓa kuma zai yi aiki tare da amsa shawarwari daga al'umma da kwamitin yanki Kwanaki 10
16 - 25 Satumba Masu nema za su yi ƙari ga neman tallafin su idan akwai bukatar hakan Kwanaki 10
26 Satumba - 10 Oktoba Amincewa da bayarwa Kwanaki 14

Oktoba-Nuwamba

Zagaye na 5: Oktoba 15 - Nuwamba 30
Kwanakin wata na Tallafin gaggawa Aiyuka Ƙiyasin lokaci
Oktoba 15 Ƙarshen lokacin miƙa tallafi
Oktoba 16-29 ubawa da mayar da martani game da neman da aka miƙa Kwanaki 14
Oktoba 30 - 8 Nuwamba Mai nema zai karɓa kuma zai yi aiki tare da amsa shawarwari daga al'umma da kwamitin yanki Kwanaki 10
Oktoba 30 - 8 Nuwamba Masu nema za su yi ƙari ga neman tallafin su idan akwai bukatar hakan Kwanaki 10
9 ga Nuwamba-22 ga Nuwamba Amincewa da bayarwa Kwanaki 14

Conversation hours

Lokutan aikin ofis
Kwanan wata Lokaci Harshe Maudu'i Irin abokin haɗin gwiwa na mai neman tallafi Mahaɗar tattaunawa
Maris 30 2022 3p.m -4 p.m UTC Turanci da Faransanci Sauye-sauye a tallafin gaggawa Masu neman Tallafin Gaggawa Mahaɗar taro a Zoom

Adireshin Taro: 874 6899 4589

Lambar sirri ta shiga taro: 454018

Afrilu 6 2022 3p.m -4 p.m UTC Turanci da Faransanci Sauye-sauye a tallafin gaggawa Masu neman Tallafin Gaggawa Mahaɗar taro a Zoom

Adireshin Taro: 874 6899 4589

Lambar sirri ta shiga taro: 454018

Afrilu 13 2022 3p.m -4 p.m UTC Turanci da Faransanci Sauye-sauye a tallafin gaggawa Masu neman Tallafin Gaggawa Taro a Zoom

Adireshin Taro: 874 6899 4589

Lambar sirri ta shiga taro: 454018