Wiki for Minorities/Minori-Ties Programme/Hausa Project

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki

Shirin Minori-Ties ya ƙunshi jerin tsare-tsare a cikin shirin Wiki don 'Yan tsiraru wato a Turance Wiki for Minorities (WfMin) an kuma shirya shirin ne domin haɓaka alaƙar zamantakewa da al'adu tsakanin ƴan ƙasashen waje (baƙi) da ƙasarsu ta asali. Kalmar ta fito ne daga kalmomi tsakanin 'yan tsiraru da alaƙa. Taimako na iya kasancewa cikin lamuran harshe, inda, alal misali, ƙungiyoyi suna ba da gudummawa tare da taimakon fasaha don haɓaka harkokin cikin gida akan Wikipedia a cikin yaren da suke magana. Hakazalika, cibiyoyi daban-daban na iya ba da gudunmawa na bayanai ko kaya (misalin kamar littattafai, mujallu, da sauransu) da za a ɗauka ko a duba su dangane da 'yan ƙasashen waje da ke zaune a ƙasashensu, domin a loda su zuwa dandalin aikinmu na wiki a ƙarƙashin lasisi na kyauta.

Cikakkun Bayanai[edit]

Ana gudanar da jerin ayyuka a duk shekara. Ayyukan Wikipedia da za ayi aiki dasu sune: WikipediaWikimedia, CommonsWikidataWiktionaryWikinewsWikisource da Wikivoyage.

Ayyuka[edit]

  • Editathons: Shirya bita kan aiyukan Wiki for Minorities a zahiri (physical) ko ta online. Yana yiwuwa a yi aiki akan Wikipedia da Wiktionary don waɗannan dalilai.
  • Ziyarci cibiyar GLAM: Editoci suna iya kai ziyara don ganin hedkwatar ƙungiyar da ke kula da 'yan ƙasashen waje ko 'yan tsirarun harshe. Amman abu na farko, ana buƙatar neman izini wannan cibiya don ɗaukar hotunan wuraren daban-daban na wannan cibiya, sannan a kimanta alaƙa tsakanin cibiyar da Editoci, a mataki na biyu kuma, a cimma yarjejeniya don yin haɗin gwiwa na dindindin: zama a cikin cibiyar, ziyartar ayyuka daban-daban don ɗaukar hoto ko ba da rahoton abubuwan da ke ciki (Wikinews na kuma taka rawa rawar gani sosai a wannan fagen).

Aukuwa[edit]

Participants[edit]