Sanarwar Tattaunawaar Gidauniya Wikimedia na tsarin shekara ta 2022/2023

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki
This page is a translated version of the page Wikimedia Foundation Annual Plan/2022-2023/Conversations/Announcement and the translation is 100% complete.

Kasance tare da Tattaunawar Tsarin Shekara-shekara na Gidauniyar Wikimedia tare da Maryana Iskander

Kuna iya samun wannan sakon da aka fassara zuwa ƙarin wasu harsuna akan Meta-wiki.

Barka,

Ƙungiyoyin Sadarwar Motsi da Dabarun gudanar da Mulki suna gayyatar ku don tattaunawa akan 2022-23 Tsarin gidauniya Wikimedia na Shekara-shekara, a tsarin rikodin ayyukan Wikimedia Foundation

Wannan tattaunawar zata cigaba tare da Maryana Iskander Babban Jami'a kuma shugaba Sauraron Gidauniyar Wikimedia.

Tattaunawar ta ƙunshi waɗannan tambayoyin:

  • 2030 Tafiyar Wikimedia da kuma jajircewa yana tsara da nuni zuwa ga "ilimi a matsayin wata cikakkiyar hidima" da "daidaitan ilimi". Gidauniyar Wikimedia tana son yin shiri bisa ga waɗannan manufofin biyu. Yaya kuke ganin ya kamata gidauniyar Wikimedia ta yi amfani da su a aikinmu?
  • Gidauniyar Wikimedia ta ci gaba da gano ingantattun hanyoyin aiki a matakin yanki. Mun ƙara mayar da hankali kan yanki a fannoni kamar grant, sabbin abubuwa, da yadda al'umma zasu tattauna. Me yake aiki da daidai/kyau? Ta yaya za mu inganta?
  • Kowa na iya ba da gudummawa ga tsarin Dabarun tafiyar. Mu tattara ayyukanku, ra'ayoyinku, buƙatunku, da darussan da kuka koya. Ta yaya Gidauniyar Wikimedia za ta tallafawa masu aikin sa kai da masu haɗin gwiwa da ke aiki a ayyukan Dabarun na wannan tafiya?

Kuna iya samun jadawalin kira akan Meta-wiki.

Za'a samu bayanin a cikin waɗansu yaruka da dama. Kowane kira za'a bada dama ga kowa don halarta. Za kuma a sami fassarar kai tsaye a wasu kiraye-kirayen.

Fatan alkhairi,