Jump to content

LGBT+ Wikimidiya/Ƙofa

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki
This page is a translated version of the page Wikimedia LGBT+/Portal and the translation is 100% complete.
Wikimedia LGBT+
Shortcut:
WM:LGBT
Wikimedia LGBT+
A User Group to support the LGBT+ community
and represent LGBT+ content
across Wikimedia projects.




Iberocoop
Iberocoop

LGBT+ Wikimidiya Kungiyar editoci ce ta Wikimidiya wacce ke bunkasa cigaban bayanaa akan Shafukan Wikimidiya dangane da ra’ayoyin al’ummomin LGBT+ da kuma tallafawa mutanen LGBT+ wadanda suke harkokin Wikimidiya. LGBT+ Wikimidiya al’ummomi ne daban daban na duniya, da ke maraba da mutane daga kowacce launin fata, addini, kabilu, kasashe, ra’ayoyin jima’i, jinsi, da kuma abubuwan da ake iya yi. An fara ambatar LGBT+ Wikimidiya ne a Wikimania na 2012 kuma Kwamitin hurdodi ta amince da ita a cikin watan Satumban 2014.

Manufa

  1. Kirkira da kuma fadada bayanai da suka shafi ra’ayin al’ummomin LGBT+ a Shafukan Wikimidiya da kuma bunkasa daukakin ingancin bayanan a kowanne harshe.
  2. Goyon bayan mutanen LGBT+ wadanda suke harkokin Wikimidiya.
  3. Samun sarari na tattaunawa akan ra’ayoyin LGBT+ a cikin dokokin Wikimidiya
  4. Karfafawa kungiyoyi don yin amfani da shafukan Wikimidiya da kuma amfani da dabi’u na ‘yantacciyar al’ada da kuma isa ga bayanai cikin sauki.
  5. Gabatar da shafukan Wikimidiya a matsayin wani abu na karfafawa al’ummomin LGBT+

Kudurori

  1. Inganta gyararraki ga kowanne ta hanyar tabbatar da cewa magance cin zarafafi da suka shafi LGBT+ ta hanyoyin dokoki masu sauki ba tare da la’akari da jinsi ba.
  2. Tabbatar da cewa dokokin rashin nuna bambanci dangane da salon jima’i, jinsi, da jima’i sun fara aiki a dukkannin shafukan Wikimidiya, da kuma shiga tattaunawa da suka shafi nuna bambanci na kowanne iri.
  3. Samar da kafofin tallafi ga al’ummomin LGBT+ da abokan su, wanda ya hada da marhaban da karfafa gwiwa daga IRC da VRT
  4. Samar da salon daukaka ƙara mai tattare da juyayi a yayin da ƙudurin shawo kan sabani bai yi aiki ba kuma mai bada gudummawa ya zabi mai sulhun LGBT+ da kan shi ko kuma mai sassantawa da ya magance matsalar
  5. Samar da muhalli mai tsaro ga masu karatun shafukan LGBT+, tare da mayar da hankali da inganta zamantakewar matasan LGBT+ a shafukan Wikimidiya.
  6. Gina babbar al’umma ga editocin Wikimidiya ‘yan LGBT+
  7. Daidaita yunkurin shafukan wiki a tsamanin WikiProject da suke aiki akan bunkasa wani bayani na LGBT+

Dabaru

LGBT+ Wikimidiya za ta tabbatar manufarta ta wadannan hanyoyin:

  1. Samar da horo ga kungiyoyi da mutane ta yadda zasu iya bayar da gudummawa ga shafukan Wikimidiya.
  2. Kirkira, tattarawa, shiryawa, da kuma gabatar da wasu na’ukan tsari wanda ke bayyana kididdigar amfani da inganci na bayanan ra’ayoyin LGBT+ a shafuka Wikimidiya.

A yayin da muke maraba da kowanne memba na LGBT+ wajen bayar da gudummawa akan bayanan ra’ayoyin LGBT+ da kan su, za’a iya cimma zangon aikin da furojet din ke nufin cikawa kawai ta hanyar idan shirye-shiryen ziyara sun tabbata don bunkasa bayanan a shashin. Aiki na gama gari zai zamana dukkannin wanda zai ilimantar da mutane akan LGBT+ a ko ina zai zamana ya rarraba bayanai a kan shafukan Wikimidiya idan kowanne wuri da suke nufin ilimantar wa suna amfani da yanar gizo a matsayin kafar samun bayanai. Idan wannan mai ilimantarwa ya bayar da wannan bayanai, to wannan mutumin zai zamana ya riski Wikimidiya LGBT+ da kuma samun horo da ya dace don samun daman yada bayanansu a kan shafukan Wikimidiya.

Sakamako

  • Karin shiga da ganin al’ummomin LGBT+ a wuraren taron Wikimdiya,ginawa akan shigowa mafi girma a wurin taron Wikimaniya.
  • Kari (budaddiyar) bayar da gudummawa daga mambobin al’ummomin LGBT+ a dukkannin shafukan Wikimidiya .
  • Daidaito tsakanin LGBT+ WikiProject.
    • Gabatarwa akan tarihi da al’adu daga GLAM LGBT+
    • Karin inganci c:Special:MyLanguage/Commons:Wiki Loves Monumentsda kwarewar mukalan LGBT+
    • Gabatar da wuraren tarihi na LGBT+ a Wiki Loves Monument
  • Ka’idojin a kan Ziyara don shawara da bunkasa dokoki a kowanne shafin Wikimidiya:
    • Chapter da kuma dokokin tsaro na wuri na WMF don tabbatar da cewa shigar a kowanne taro don tabbatar da cewa an dauki matakin da ya dace a kan lokaci a kan kowanne korafi na budaddiyar cin zarafi na LGBT+
    • Jagoranci ga kowanne sabbin editocin LGBT+ (da wadanda ke gyara shafukan LGBT+) a kan yadda zash kare kansu kuma su nemi taimako a lokacin da bukatar hakan ta tashi.
    • Hanyoyi masu sauki don mayar da martani ga cin zarafi da suka shafi LGBT+ ko barazana a kan kowanne shafi na Wikimidiya da IRC.
  • Isa ga wani taimako na LGBT+ a kan wiki, IRV da kuma ta imel (misali, samu isa ga kowanne memba da aka tantance na VRT zuwa ga lgbt(_AT_)wikimedia.org).
  • Nazari da bincike na kai tsaye daga kwararru a kan shafukan Wikimidiya da kuma Gidauniyar Wikimidiya a wajen magance matsaloli na kyama da cin zarafi.
  • Biyan kudi don duba da bayanan kididdiga a kan shiga shafukan LGBT+ da kuma hange akan yanayin gyara don goyon bayan shirye-shiryen da aka tsara.
  • Samfuri don marasa galihu na gaba masu kungiyoyi.

Ayyuka

Ayyukan da suka shafi LGBT+ Wikimidiya:

hadin gwiwa da shafukan Wikkmidiya da kuma kungiyoyin waje, irin su WikiProject Nazarin LGBT (Wikipedia ta Turanci), LGBT Free Media Collective (Wikimedia Commons), da kuma Wiki Loves Pride.

Sasanci

Sadarwa