Jump to content

Haramtawa na duk duniya

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki
This page is a translated version of the page Global bans and the translation is 100% complete.

Haramtawa na duk duniya' hani ne a hukunce na yin gyara ko samun alfarma (misali amfani da imel na musamman wato "Special:EmailUse) a dukkannin Shafukan Wikimidiya. Yana bayyana fayyacaccen yarjejeniya mai fadi na al’unma. Haramtawa na duk duniya ba wai wani nau’i bane na hukunci, ba wai kuma an yi shi ne don samar da “nutsuwa ba” na lokaci ba. Haramtawa na duk duniya an yi shi ne don bada kariya ga Shafukan Wikimidiya a yayin da wata kungiya ba za ta iya shawo kan matsalar ba ta hanyoyin dakatarwa masu sauki, kuma a dalilin hakan yana zamantowa na dundundun.

Ana sanya haramtawa na duk duniya musamman a yayin da kungiyoyi daban daban sun zabi a kange wani edita a dalilin wani nau’i na batanci. Shafukan Wikimidiya baki daya sun kasance masu jagorantar kawunan su ne. A dalilin haka ana kyautata zato a yayin da wani edita ya zabi ya zamo mamba na wata kungiya, ba tare da la’akari da tarihin sa a wani shafi ba. A dalilin haka, ba zai yiwu a yi haramtawa na duk duniya ba a yayin da kawai aka hana edita gyara na wucin gadi, ko kuma kawai an kange shi ne daga gyara shafi guda daya. Ku tuna cewa, haramtawa na duk duniya, hani ne na gyara kowacce shafi a fadin duniya kuma ba kasafai yake faruwa ba.

Kada a kuskure haramtawa na duk duniya da kullewa na duk duniya, tsari a fasahance na hana adireshin IP ko kuma jerin su (kamar, editocin da basu yi rijista ba) daga gyara Shafukan Wikimidiya, sai dai Meta-Wiki. Wannan doka ta kunshi kawai haramtawar gyara na duniya wanda kungiyoyin al'umma ke bayar wa. Gidauniyar Wikimidiya tana da ikon haramtawa ko waye gyara a duk shafukan ta na duniya, sannan kuma Dokar WMF akan Haramtawa na duk Duniya ne ke kula da wannan wannan haramtawa.

Rabe-Raben Haramtawa na duk Duniya

Ana la'akari da haramtawa na duk duniya ne a lokacin da aka cika dukkan ka'idoji masu zuwa:

 1. Mai amfani da shafi ya cigaba da nuna wani nau'i na batanci a shafuka dabab-daban wanda ba kawai dan karamin batanci bane ko banzatarwa. Ba'a bukatan haramtawa na duk duniya akan matsalalolin da ba'a tantance su ba akan batanci ko bazatarwa, tunda za'a iya magance wannan ta hanyar kangewa ko rufewa (wanda masu kula da gyare-gyare ka iya yi ba tare da bukatar wani dogon bayani ba). Duba bukatar zama mai kula da shafuka/na duniya.
 2. Anyi wa mai amfani da shafin bayani sosai akan akan hanyoyin da suka dace na fafatawa a wannan Shafin, kuma an bashi dama da ya dace don gyara wadannan matsaloli. Dole ne wadannan shafuka su nuna kyautata zato da kuma bayyana halaye da ayyuka masu kyau da suka jibanci kudurinsu da burukansu. Wannan tsari ya shafi nunawa masu amfani da shafin abubuwan da ake tsammani daga gare su, an basu dama daidai gwargwado don shawo kan matsalolinsu, kuma suka zabi cewa bazasu bi wadannan ka'idoji ba yadda ya dace.
 3. An kulle ko an haramtawa mai amfani da shafin daman gyara a shafuka biyu ko fiye da hakan. Dole ne wadannan kullewa ko haramtawa su kasance a dalilin halayya na batanci na mai amfani da shafi, kuma basu shafi kullewa na kariya ba kamar kullewar da babu komai akan masu amfani da shafi da basu da gyara ko daya, da kuma kullewa akan matsalar tsaro na asusun mai amfani ko kuma sunan mai amfani da yake bada matsala.

Cike wadannan ka’idoji kawai ba ya nufin cewa ana bukatan haramtawa na duk shafuka. Abubuwan da suka gabata na bukatar haramtawa na duka shafuka sun hada da:

 • Cin zarafi ko kuma tsoratar da masu bada gudummawa akan wani shafi, a kan Wiki ko kuma a waje.
 • Zamba mai tsanani a kan wiki ko kuma satar asali wanda ba cin mutuncin asusu bane mai sauki.
 • Wuce gona da iri a wajen amfani da ikon amfani don isa zuwa ga bayanai na sirri, irin su duba masu amfani da shafi ko kuma masu bin diddigi.
 • Keta hakkoki na dokokin sirri ko kuma wasu dokokin Wikimidiya.
 • Yawaita keta hakkokin mallaka a shafuka daban danan.

Dangantaka da dokoki na gida

Wannan manufofin an yi su ne don haɓaka manufofi da hanyoyin da ke akwai na daukakin shafuka, ba wai don su wanzu a matsayin maye sun gurbin ba. Dukkanin tsarin warware rikice-rikice ya kasance alhakin kowane al'umma, kuma wannan tsari ba wuri ne don nishaɗin shawarwari don hana ko toshe mai amfani a kan aikin guda ba.

Dangantaka dlga Ka’idojin Amfani

Ka’idojin Amfani na Wikimidiya, wadanda suke wajaba daidai da sauran shafukan ta, yana nuni a takaice dangane da wadannan dokoki da kuma amincewa da dakatar da masu amfani da shafuka wanda ke keta ko dai wadannan ka’idoji da kansh ko kuma wasu dokokin da ka’idoji na al’umma wajibai. A matsayin masu samar da sabis na shafukan Wikimidiya, Gidauniyar Wikimidiya tana da kuma zata cigaba da goyon bayan yarjejeniyoyi da al’ummomi ke yankewa dangane da dakatarwa da kuma haramtawa.

Amsar yarjejeniya a akan haramtawa na duka shafuka

Ayyukan masu sauƙi.

Ana gudunar da tattaunawa akan haramci na duk duniya ta hanyar bukaci tsokaci a shafin Meta. Ana iyawa amincewa da haramtawa na duka shafuka a yayin da mai amfani da shafi ya gabatar da bayyananniyar cutarwa kuma na yanzu a dukkannin shafukan Wikimidiya, ana amincewa ne da wannan hukunci ne ta hanyar tattaunawa mai zurfi kuma bayyananne da adalci wanda zai wakilci mafi akasarin ayyukan Wikimidiya, kuma za’a tabbatar da kulawa mai kyau na matsaloli da damuwa da kan iya tasowa a dalilin wannan mataki. A yayin fara tattaunawa akan ko akwai hujja ta cutarwa ga dukkanin al’ummomi kuma a tabbatar da haramtawa na duka shafuka, a taimaka a bi wadannan hanyoyin:

 1. A tabbar da cewa mai amfani ya cike duka sharuddan haramtawa na duka shafuka kafin a bude shafin tattaunawa.
 2. A bude sabon shafin bukatar tsokaci a Meta. Gabatarwar ta dauki sunan mai amfani da shafi da za’a tattauna akan haramta masa bude duka shafukan Wikimidiya. Dole ne mai gabatarwar ya gabatar dukkanin al’amurran da suka dace da sharuddan haramtawa na duk duniya ba tare da son ra’ayi ba. Dole ne kuma mai gabatar da korafi ya yi yinkurin nuna cewa rashin bada gudummawa yadda ya dace da wannan da ake korafi akai zai janyo babban matsala ga dukkannin al’ummar Wikimidiya.
 3. A sanar da wanda ake korafi akan shi a kan game da tattaunawar a dukkannin shafukan da yake bada gudummawa. Idan an rufe wannan edita da aka tsayar da tuhumar haramta masa shiga dukkannin shafukan Wikimidiya daga gyara a Meta, za’a iya amincewa da bude shi na wucin-gadi don bashi dama wajen shiga tattaunawar.
 4. A sanar da dukkannin kungiyoyin al’umma da wannan edita ke mu’amala da su akan wannan tattaunawar ta sananniyar hanya da aka fi sani. A tabbata an tsaya tsaka-tsaki ba tare da tuhuma ta cin zarafi ba, wacce ba daidai ba, ko kuma wuce gona-da-iri wajen yin tsokaci.

Duk tattaunawar da ta kasa bin wadannan matakai na sama an soke ta, kuma za’a yi gaggawar rufe ta. Bugu da kari, dole ne edita ya:

 1. kasance yana da asusu a Wikimidiya; kuma
 2. ya kasance ya yi rijista fiye da watanni shida kafin bukatar tattaunawar; kuma
 3. ya kasance yana da akalla gyararraki 500 a dukkannin shafuka (na shafukan Wikimidiya).

Da zarar buƙata mai inganci don sharhi ya samar da cikakkiyar yarjejeniya, mai kula da shafuka wanda bashi da alaka da tattaunawar ko ra’ayi na iya rufe tattaunawar. Tattaunawar ya kamata ta kasance a buɗe aƙalla makonni biyu, amma ba fiye da wata ɗaya ba. Masu kula na iya fadada tattaunawar a yanayi na musamman. Ana iya rufe buƙatar tattaunawar ba tare da tattaunawa mai zurfi ba lokacin zancen ya kasance ba mai inganci ba. Ana iya rufe bukatar tattaunawar bayan tattaunawa mai zurfi lokacin da ba za a iya cimma yarjejeniya ba.

Tattaunawa a harsuna daban daban

Da fatan za a san cewa za'a iya tattaunawar kuma ya kamata a gudanar da ita a cikin harshen da ya dace ko harsunan da suka dace kowane shafi da mai amfani ya kasance yana aiki. Shafukan Wikimidiya sun wanzu a cikin daruruwan harsuna, kuma ta haka ne ya kamata a ba da al'ummomi daban daban damar shiga cikin tattaunawar duniya ba tare da la'akari da kwarewar su a sauran harsunan ba. A lokuta inda babu mutane masu fassara, fassarar inji na iya aiki a matsayin maye gurbin sadarwa tsakanin al'ummomi.

Kaddamar da haramtawa ta duka shafuka

Haramtawa na duka shafuka a hukumance ta kore duk wata alfarma a dukkannin shafukan Wkkimidiya, ko da kuwa an hada asusu ta hanyar kafar sadarwa hadadde. Duk wani yunkuri na shawo kan haramtawa na duka shafuka ya zama saba dokar Ka'idar Amfani, ba tare da la'akari da kowanne asusu ne aka yi amfani da shi ba. Haka zalika, ya kamata a sanar da kungiyoyin al'umma na gida da aka haramtawa wannan edita yin gyara a wata sananniyar kata ta jama'a akan wannan hukunci. Masu kula da shafuka kuma suna iya yanke hukuncin daukan mataki wajen amsa bukatu na rufe duk wata asusu da ake kyautata zato wannan edita da aka haramtawa shiga dukkannin shafukan Wikimidiya na amfani da su.

Idan hukuncin ya bukaci matakai daga masu kula da shafuka, ya kamata a bukaci masu kula da shafuka. Kuma a saka mahada zuwa ga shafin tattaunawa a tattare da bukatan ku; idan ba haka ba kuwa za'a yi watsi da ita a dalilin rashin yarjejeniya.

Canza matakin haramtawa na duk duniya

Ana gudanar da tattaunawa na canza matakin haramci na duka shafuka ta hanyar bukatar tsokaci a shafin Meta, don a bada damar mutane da yawa da zasu halacci tattaunawar. Dole ne a bi hanyoyin yarjejeniya na bukatar haramtawa, wanda aka bayyana a sama.

Duba nan