Movement Charter/Abubuwan da ta kunsa/gabatarwa

From Meta, a Wikimedia project coordination wiki
This page is a translated version of the page Movement Charter/Content/Preamble and the translation is 78% complete.
Outdated translations are marked like this.


Ƙungiyar Wikimedia ta mayar da hankali ne akan ƙirƙirar haɗin gwiwa, kulawa, da kuma fadada samun ilimi kyauta a duniya. Yunkurin ya ƙunshi: masu gyara, mahalarta, ayyuka, alaƙa, cibiyoyi, wuraren fasaha, Gidauniyar Wikimedia, da sauran abubuwan da ke yanzu da na gaba.

Kungiyar yarjejeniya ta Wikimediya (“charter”) tana wanzuwa ne don ayyana Kungiyar Wikimedia, muhimman hakkokin ta da kuma ka’idojin ta. Ta kasance yarjejeniya ce a hukumance wacce ke bayyana dangataka a tsakanin daukakin masu hannun jari a kungiyar, da kuma hakkokin su da kuma ayyukan su. Wannan ya shafi duk wani bangarori da ke wakana da kuka wasu wanda za’a kirkira a nan gaba.

Membobin al’ummomin mu daga kasashe da dama ne suka tsara wannan Yarjejeniya, daga shafukan Wikimedia daban daban. Amincewar al’umma dangane da wannan Yarjejeniya sun faru ne a cikin hanyoyi da aka tsara. Sun wanzu akan daukakin kungiyar. Movement Charter ta shafi daukakin masu bada gudummawa, bangarori da kuma wurare na fasaha a tsakanin Kungiyar Wikimedia. Har wayau ta shafi wuraren da ba kan wiki ba wanda a hukumance suna da alaka da bangorin kungiyar.

A tsakanin kungiyar akwai jerin shafuka da dama wadanda za’a iya yin gyara acikinsu (“Shafukanmu”) zuwa harsuna da dama tare da manufofi daban daban. Shafukan sun kasance mafi yawa masu tafiyar da kansu ne, dangane da bayanan da ake kirkira, kula da bayanai, da kuma dokokin al’umma. Wasu bangarorin ba’a kula da su ta hanyar tafiyar da kansu, amma bangarori daban daban ke kula da su a yayin da ba’a iya aiki a kansu a gargajiyance. Wadannan bangarori sun hada da, amma ba’a iyakance su da: shafi a daukakin ta; kungiyar; ita Gidauniyar Wikimedia; da kuma Majalisun Duniya. Kowanne bangare ya yi aiki a matakin da ke kusa da masu bayar da gudummawa, a yayin da ta kama. Kungiyar har ila yau zata kunshi gabaki daya kungiyoyin da aka tantance da wanda ba’a tantance ba wanda suke mayar da hankali akan wani batu guda daya ko kuma yankin kasashe. Aikin wadannan kungiyoyi ahine tallafawa shafuka kai tsaye ko kuma ba kai tsaye ba.

Dan ƙarin taimako ga wadannan shafuka ko kungiyoyi akwai wani cikakken kayan aiki wanda ke taka rawa daban daban, wanda suka hada amma ba iyakacinsu ba kenan:

  • Tallfawa bukatu na fasaha ga kungiyar da kuma masu karanta bayanan ta, wanda suka samar su ne:
    • Gidauniyar Wikimedia
    • Rassan da ke da ra’ayi
    • Wanda suka karfi tallafi da kuma masu kongiragi da ke aiki akan wani shafi na fasaha
    • Masu bunkasa gudummawa, wanda ke aiki a MediaWiki extension, rubuce-rubuce ga shafukan gida, tallafi ga shafukan duniya
    • Softwayar tallafi ta fasaha ta musamman (misali, (Phabricator)
    • Masu samarwa na waje (misal, GiHub)
  • Bayar da tallafin kudi da sauran ababe don bungasa tafiyar da da kuma ajiyar ilimi, wanda suka hada da:
    • Tara kudi wanda WMF ku gudanarwa, Wikimedia Endowment, Wikimedia Enterprise, da kuna rassan mu. Wannan ma ya hada da nema, amsa, da kuma kula da tallafin grant da kuma kongilolo daga bangarorin waje
    • Tallafawa don bunkasa dabaru da kuma gina iya aiki, wanda Gidauniyar Wikimedia ke samar wa, rassan mu, kungiyoyin al’umma, da kuma masu bayar da gudummawa a tsakanin shafuka
    • Ka’idoji, hanyoyi da kuma tsaruka da suka jibance kowanne rassa, wanda su kansu rassan ke kula da su, ma’aikatan su da kuma masu bayar da gudummawar a cikinsu (wanda suka hada da membobin majalisa, idan akwai su?
  • Bunkasa muhalli mai kariya kuma mai amfani inda za’a rika yada ilimi kuma a same su, inda yake da wuya ga shafukan cikin gida su yi hakan da kan su sun hada da:
    • Ka’idoji, hanyoyi da kuma tsare-tsare da suka shafa na duniya, wanda kungiyar al’ummomi na duniya da Gidauniyar Wikimedia ke kula da su
    • Ka’idoji, hanyoyi da kuma tsare-tsare da suka shafi shafuka daban daban, wanda shafukan da kuma masu bayar da gudummawa ke kula da su
    • Tsare-tsare da ke tallafa wa masu amfani da kuma masu bayar da gudummawa wajen samun kariya, ta hanyar mutane da kuma kayan fasaha
    • Tallafin doka ga kowanne mai amfani da shafin, da hadin gwiwa da rassan gida
    • Goyon bayan sauyin doka da tsare-tsaren da zasu kawo manyan damamaki da kariya ga isa ga ilimi kyauta

Wadannan tallafi na kayan aiki sun ta’allaka ne akan iyakokin da ke waje da kungiyar. Haka zalika, dole ne tallafib ya zo daidai da ka’idojin mu da kuma harkokin kungiyar